Podcast charts
Published by ADPlusHausa | Podcast
Sashen podcast na Afrika 🎙 Fagen tattaunawa…Batutuwa da suka shafi al'adu… Muna bawa mazauna Afrika masu magana da harshen Hausa muhimmanci a dukkan lamuran rayuwarsu…Shiri ne da ke karkashin kafafen sadarwa na Afrika.
On the charts
Every published chart this podcast appears in, in the snapshot behind this page. Each one links to the chart it came off.
From the feed
The latest episodes published to this podcast’s own RSS feed. Titles and descriptions are the publisher’s.
IYALI SU NE GINSHIƘIN AL’UMMA; IDAN GIDA YA GYARU, AL’UMMA MA ZA TA SAMU GYARA. GINA IYALI NAGARI BA YA TSAYAWA GA SAMUN KUƊI KO ZAMA TARE KAWAI, A’A, YANA BUƘATAR SOYAYYA, FAHIMTAR JUNA, MUTUNTA JUNA, HAƘURI, AMANA DA KYAKKYAWAR TARBIYYA. A YAU ZA MU TATTAUNA MUHIMMAN RUKUNAN DA AKE BUƘATA WAJEN GINA IYALI NAGARI, DA KUMA WASU ƘALUBALEN DA KAN KAWO RASHIN JITUWA TSAKANIN MA’AURATA DA SAURAN ’YAN UWA. BABBAN BAƘO: MAL. LAWAN ADAM GIGINYU, MASANIN KIMIYYAR ZAMANTAKEWA A NAKJERIYA. MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA.
“Shugabanci na Gari a Tsarin Dimokuraɗiyya.” Shugabanci ba mulki kawai ba ne, illa amana ce, nauyi ne, da kuma hidima ga jama'a. A tsarin dimokuraɗiyya, ana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu, amma tambayar ita ce: ta yaya za mu tabbatar da cewa wannan zaɓe yana haifar da shugabanci mai adalci, gaskiya, amana da bin doka? A yau za mu duba ginshiƙan shugabanci na gari, rawar shugabanni da jama'a, da kuma manyan ƙalubalen da ke hana samun kyakkyawan shugabanci a Najeriya da Afirka.
A yau mutane da dama suna son su zuba jari domin su ƙara samun kuɗi, amma rashin ilimi yana sa wasu su yi asara ko kuma su faɗa cikin hanyoyin da ba su dace ba. A wannan shiri na Rumfar Africa Podcast Hausa, kashi na (55) za mu tattauna muhimman ƙa'idojin da ya kamata kowane mai son zuba jari ya sani, tare da ƙwararren masani a fannin tattalin arziki, zuba jari da Islamic Finance, Dr. Nabil Bello Sa'id, Manajan Darakta na Konooz Investments. Ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshe, domin wataƙila wannan tattaunawa za ta canja yadda kuke kallon zuba jari baki ɗaya. Domin neman karain bayani a Konooz Investments:- +2347063829915 | +2349069968666 | +2349015995200
MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO?Domin yin nazari a kan wannan batu, muna tare da babban baƙonmu, Farfesa Munir Abdullahi Kamba, wanda zai yi mana bayani kan tushen wannan matsala, illolinta, da kuma hanyoyin da matasa za su bi wajen gina arziki cikin hikima da dorewa.
Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya? -------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene ne mafita? Kuma wane tasiri wannan rikici zai iya yi ga tattalin arzikin duniya, tsaron ƙasashe, har ma da rayuwar al'ummar Afirka? A wannan shirin na Rumfar Africa Podcast Hausa, za mu yi nazari cikin natsuwa tare da baƙo na musamman domin fahimtar tushen rikicin, matsayinsa a siyasar duniya, da hanyoyin da za su iya kai ga zaman lafiya.
TAKAITACCEN SHARHI A KAN ABINDA KE WAKANA A KASHEN SAHEL, TARE DA MASANIN KIMIYYAR SIYASA DA SHA'ANIN MULKI
Da’awar Musulunci da Bible: Hanyoyin Isar da Saƙon Musulunci ga Mabiyan Kiristanci.Ta yaya Musulmai za su yi da’awa cikin hikima da fahimtar addinin Kirista? Wane matsayi Bible take da shi a tattaunawar addinai? Kasance tare da mu domin jin tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin gina fahimta, mutunta juna da kuma isar da saƙon Musulunci cikin basira da hikima.
“HAJJI: MAKARANTAR SHUGABANCI” Shin wane darasi shugabanni da al’umma za su koya daga hajji? Ta yaya hajji ke koyar da tsari, adalci, tawali’u da haɗin kai? Domin tattauna wannan batu, muna tare da babban bako:IMAM, DR. MUHAMMAD SULAIMAN ADAM.
Sana’ar Jari Bola ta zama ɗaya daga cikin sana’o’in zamani da suka mamaye duniya, tana jan hankalin miliyoyin mutane saboda damar samun riba cikin gajeren lokaci. Amma a bayan nasara akwai ƙalubale, haɗari da dabarun da ke buƙatar ilimi da ƙwarewa. A wannan shiri na musamman, za mu tattauna kan nasarorin sana’ar, ƙalubalen da masu ita ke fuskanta, hanyoyin inganta ta a wannan zamani, da kuma yadda ake gudanar da sana’ar jari bola a sassa daban-daban na duniya. Kasance tare da babban bako, Aliyu Sabo Yakasai, fitaccen mai sana’ar jari bola, domin jin sirrika, gogewa da muhimman darussa masu ɗaukar hankali!
A WANNAN KASHI NA 49, MUN TATTAUNA YAKIN KWANAKI 12 TSAKANIN ISRA’ILA DA IRAN: • ASALIN RIKICIN. • TARIHIN KAFUWAR ISRA’ILA DA IRAN. • YADDA DANGANTAKA TA DIFLOMASIYYA TA RIKIDE ZUWA GABA DA ADAWA. • ME YA TAYAR DA RIKICIN YANZU. • RAWAR KASASHEN YAMMA WAJEN TALLAFAWA ISRA’ILA. • DA TASIRIN RIKICIN A NAHIYAR AFRIKA. TARE DA BABBAN BAKO: DR. RIYA’UDDEEN ZUBAIR MAITAMA — ƘWARARRE A KIMIYYAR SIYASA DA SHA’ANIN MULKI, KUMA MALAMI A JAMI’AR BUK KANO. SHIRIN NA CIKE DA BAYANAI MASU ZURFI DA FAHIMTAR ABUBUWAN DA KE FARUWA A DUNIYAR SIYASA. #podcastclips #Hausa #duniya #siyasa
TATTAUNAWA MAI ARMASHI KAN GWAGWARMAYAR DA’AWA GA WAƊANDA BA MUSULMI BA — MUSAMMAN KIRISTOCI DA MAGUZAWA.ZA MU BINCIKO NASARORI, ƘALUBALE, DA HAƊURRAN DA KE TATTARE DA WANNAN AIKI MAI MUHIMMANCI.BABBAN BAƘONMU A SHIRIN: SH. IMAM ADAM IDRIS DUMI, SHUGABAN ƘUNGIYAR ƘWARARRUN MASU DA’AWA, RESHEN JIHAR BAUCHI, WANDA YA SHAFE SHEKARU YANA GUDANAR DA WANNAN DA’AWAR CIKIN ƘWAREWA DA JAJIRCEWA.
SHIRIN ZAI YI WAIWAYE NE A KAN TARIHIN GWAGWARMAYAR KAFUWAR KUNGIYAR IZALA, NASARORI DA KUMA KALUBALEN DA TAKE FUSKANTA, DA KUMA BADA SHAIDA A KAN DALILIN RABUWAR IZALA, TARE DA JIGO A KUNGIYAR SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA.BATUTUWAN SHIRIN:
SHIRIN ZAI YI WAIWAYE NE A KAN TARIHIN GWAGWARMAYAR KAFUWAR KUNGIYAR IZALA, NASARORI DA KUMA KALUBALEN DA TAKE FUSKANTA, TARE DA JIGO A KUNGIYAR SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA. Kuna iya sauraron shirin ta hanyar dandamalinmu na podcast ta wayar hannu. Muna ba da shawarar sauraron Podcast din ta hanyar manhajar Apple Podcasts akan iPhone, da manhajar Google Podcasts akan Android.Muna son ku dinga bayyana mana ra`ayoyinku game da shirye-shiryen, za kuma ku iya ba mu maki game da Podcast din akan Apple Podcast. Hakanan kuma kuna iya ba da shawarar baƙon da za mu tattauna da shi a podcast din (RUMFAR AFRICA PODCAST) ta hanyar aiko mana da emel a:
#hausa #podcast #interview Kuna iya sauraron shirin ta hanyar dandamalinmu na podcast ta wayar hannu. Muna ba da shawarar sauraron Podcast din ta hanyar manhajar Apple Podcasts akan iPhone, da manhajar Google Podcasts akan Android.Muna son ku dinga bayyana mana ra`ayoyinku game da shirye-shiryen, za kuma ku iya ba mu maki game da Podcast din akan Apple Podcast. Hakanan kuma kuna iya ba da shawarar baƙon da za mu tattauna da shi a podcast din (RUMFAR AFRICA) ta hanyar aiko mana da imel a: hausaadp@gmail.com
A KARO NA FARKO A KAFOFIN YADA LABARAI, LABARIN MALAMIN DA AKA TSARE A GIDAN YARI NA TSAWON SHEKARA 3 A KAN TUHUMAR BOKO HARAM, KUMA ZA KU JI ABINDA YA FARU DAGA BAKIN SA.
TATTAUNAWA A KAN AIKIN AGENT MATSALOLINSA DA HANYOYIN MAGANCE SU, DA KUMA ALAKAR AGENT DA HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA NAJERIYA (NAHCON), TARE DA SHUGABAN KAMFANIN MAIKAHO TRAVEL AGENT, KANO.
SHIRI NA MUSAMMAN AKIN LABARAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A IKIN HAJJI TSAKANIN JIYA DA YAU
SHIRI NA MUSAMMAN AKIN LABARAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A IKIN HAJJI TSAKANIN JIYA DA YAU
SHIRIN ZAI GAYYATO MUKU MAHADDATA MAKARANTA AL-QUR'ANI DON JIN YA SUKA HADDACE AL-QUR'ANI DA KUMA ALAKAR SU DA SHI, A CIKIN SALO NA TATTAUNAWA MAI BAN KAYE, A KULLUM A CIKIN WATAN RAMADAN.
SHIRIN ZAI GAYYATO MUKU MAHADDATA MAKARANTA AL-QUR'ANI DON JIN YA SUKA HADDACE AL-QUR'ANI DA KUMA ALAKAR SU DA SHI, A CIKIN SALO NA TATTAUNAWA MAI BAN KAYE, A KULLUM A CIKIN WATAN RAMADAN.
Ranking source
Apple Podcasts rankings via the Mato Topic Intelligence Platform.
Observed September 20, 2026.
Apple and Apple Podcasts are trademarks of Apple Inc., registered in the U.S. and other countries.
Pairs with
Bring this source into Mato to read its transferable patterns, then turn them into an original show for your own audience.